Yayin da Manzon Allah SAW ya shiga Madina a cikinta kowane abu ya haskaka, kuma Ranar da ya rasu a cikinta kowane abu a cikinta yayi duhu

Yayin da Manzon Allah SAW ya shiga Madina a cikinta kowane abu ya haskaka, kuma Ranar da ya rasu a cikinta kowane abu a cikinta yayi duhu

Daga Anas Bin Malik -Allah ya yarda da shi- ta ce: "Yayin da Manzon Allah SAW ya shiga Madina a cikinta kowane abu ya haskaka, kuma Ranar da ya rasu a cikinta kowane abu a cikinta yayi duhu, kuma bamu watsa kasa kan Kabarin Manzon Allah SAW da Hannayenmu, kuma Mu wajen rufeshi har sai da muka tsani Zukatanmu"

[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi]

الشرح

Anas Bin Malik yana bada Labari daga Manzon Allah SAW cewa shi yayin da ya shiga Madina Farkon Hijirasa daga Makka, komai ya haskaka, yayinda da kuma ya yi wafati komai yayi duhu kuma Duhun da Hasken da aka faxa a wannan Hadisin ana nufin na Ma'ana bana Zahiri ba, sannan ya ya bada labarin cewa yayin suka gama binneshi basu samu zukatansu kamar yadda suke ba a baya a lokacin Manzon Allah SAW yana raye, na hasken Imani da Tausayi da Haxin kai a tsakaninsu saboda yankewar Wahayi, da rashin Albarkar Zama da shi SAW.

التصنيفات

Wafatinsa SAW