Manzon Allah SAW bai bar Dinare da Dirhami ba ko Akuya ko Raqumi kuma bai yi Wasiyya da komai ba

Manzon Allah SAW bai bar Dinare da Dirhami ba ko Akuya ko Raqumi kuma bai yi Wasiyya da komai ba

An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda fa ita- ta ce: "Manzon Allah SAW bai bar Dinare da Dirhami ba ko Akuya ko Raqumi kuma bai yi Wasiyya da komai ba"

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- tana bada labarin cewa Manzon ALlah SAW bai bar komai ba bayan Mutuwarsa kaxan ne ko mai yawa, kuma bai bar Akuya ba, ko kuma Raquma ko wanin hakan na dangogin Dukiya, Kuma bai yi wasiyya da wani abu ba, tana nufin Wasiyyar Kuxi na Musamman; Saboda Mutum yana iya yin Wasiyya ne idan za'a gajr shi, kuma shi SAW bai bar komai na Gadon ba da za'a gada ballantana yayi wasiyya a cikinsa, Kuma Haqiqa Manzon Allah SAW yayi wasiyya da wasu abubuwan daban, daga cikinsu akwai kula da Sallah, da kuma futar da Yahudawa da nasara daga Jazirar Larabawa

التصنيفات

Wafatinsa SAW