Shin ba zan gaya muku game da rukunoni uku ba: Daya daga cikinsu ya koma ga Allah, kuma Allah Ya ba shi. Shi kuma dayan,sai yaji kunya sai Allah ya ji kunyarsa, amma dayan sai ya bujure sai Allah ya kau da kan ga barinsa

Daga Abu Waqid al-Harith bin Auf - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da yake zaune a cikin masallaci, kuma mutane suna tare da shi, kamar yadda mutane uku suka zo, sai biyu suka zo wajan Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai daya ya tafi, ya tashi tsaye A kan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Amma dayansu, sai ya ga wani rata a cikin zobe ya zauna a ciki, dayan kuma ya zauna a bayansu. Na uku, ya yi nasarar tafiya. Lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya gama ya ce: "Shin ba zan gaya muku game da rukunoni uku ba: Daya daga cikinsu ya koma ga Allah, kuma Allah Ya ba shi. Shi kuma dayan,sai yaji kunya sai Allah ya ji kunyarsa, amma dayan sai ya bujure sai Allah ya kau da kan ga barinsa

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi, Ladaban Malami da Xalibi