Sallar jam'i ta fi sallar mutum shi kadai da daraja ashirin da bakwai.

Sallar jam'i ta fi sallar mutum shi kadai da daraja ashirin da bakwai.

Daga Abdullah Dan Umar -Allah ya yarda da su- zuwa ga Annabi: "Sallar jam'i ta fi sallar mutum shi kadai da daraja ashirin da bakwai

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Wannan hadisi yana bayani akan falalar sallar jam'i akan sallar mutum shi kadai,cewa abin da ke cikin fa'idojin sallar jam'i da maslahar jiki- ya wuce na mai yin salla shi kadai da lada ashirin da bakwai, ba makawa wanda ya yi asarar wannan riba mai girma ya yi babbar asara