na kwana a wajan Gwaggwona Maimuna,sai Manzan Allah ya tashi yana salla da daddare,sai na tsaya a hagunsa,sai ya ruko kaina ya tsayar dani a damansa

na kwana a wajan Gwaggwona Maimuna,sai Manzan Allah ya tashi yana salla da daddare,sai na tsaya a hagunsa,sai ya ruko kaina ya tsayar dani a damansa

an karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah ya yarda dasu yace: "na kwana a wajan Gwaggwona Maimuna,sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya tashi da daddare yana salla,sai na tsaya a hagunsa.sai ya ruko kaina ya tsayar dani a damansa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Sahabi maigirma dan Abbas Allah ya yarda dasu ya bada labari cewa ya kwana a wajan Gwaggwonsa matar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, don yai tsinkayi da kansa yadda tsayuwar daren Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi take yayin da Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya tashi da daddare, sai dan Abbas ya tashi don yai salla tare dashi, sai ya zama a hagun Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi a matsayin mamu;saboda cewa dama ita tafi kuma itace wajan tsayuwar mamu daga liman in ya kasance shi kadai ne sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ruko kansa, ya jawo shi ta bayansa,sai ya tsayar dashi a damansa

التصنيفات

Tsayuwar Dare