"Ya Ubangiji Mai renon Mutane, mai tafiyar da cuta, ka warkar kaine mai warkawa, babu mai warakarwa sai kai, warakarwar da bata barin cuta"

"Ya Ubangiji Mai renon Mutane, mai tafiyar da cuta, ka warkar kaine mai warkawa, babu mai warakarwa sai kai, warakarwar da bata barin cuta"

An rawaito daga Anas -Allah yayarda da shi- cewa shi ya ce da Sabit -Allah ya yi masa rahama: bana yo maka Rukya ba da rukyar Manzon Allah -Amincin Allah a gareshi-? ya ce E , yace: "Ya Ubangiji Mai renon Mutane, mai tafiyar da cuta, ka warkar kaine mai warkawa, babu mai warakarwa sai kai, warakarwar da bata barin cuta"

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Lallai cewa Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- ya kirawo Sabit Al-Bunani kuma ya ce da shi bana yi maka Ruqya ba da Ruqyar Manzon Allah SAW ya kasance yana roqon Ubagijinsa ga Mara lafiya kan ya yayewa mara lafiyar tsananinsa da raxaxinsa kuma ya sanya shi waraka da babu wata Waraka bayanta, kuma Malamai sun haxu kan halacin Ruqya idan ta haxa abubuwa uku: 1- ta kasance da zancen Allah aka yi ta ko sunayensa ko Siffofinsa, 2-kuma ta kasance da Yaren Larabci ko kuma da abunda za'a iya gane Ma'anarsa, kuma anso ta Kasance da Lafazan da suka zo a cikin Hadisisai 3-kuma mai yin Ruqya xin ya qudurce cewa Ruqyarsa ba ba zatayi tasiri ba ita kaxai sai da qudurar Allah SWT

التصنيفات

Hukunce Hukuncen Ruqiyya, Ladaban duba Mara lafiya