Madina Harami ce tsakanin Dutsen Eir har zuwa Dutsen Sauru, sabda haka duk wanda ya farar da wata Barna a cikinta, ko ya boye wanda ya farar da ita, to La'antar Allah ta tabbata a gare shi da Mala'ikun Allah da Mutane baki daya, Kuma Allah ba zai karbi komai daga gare shi ba na tuba ko kuma na fansa

An rawaito daga Yazid Bn Sharik Bn Tarik, ya ce: naga Ali -Allah ya yarda da shi- akan Minbari yana huduba sai naji shi yana cewa: Aa Wallahi bamu da wani littafi da muke karantawa sai Littafin Allah da abin da yake cikin Takarda sai ya budeta sai gashi a cikinta akwai: Hakoran Rakumi, da wasu abubuwa na Mikuna, kuma a cikinta Manzon Allah ya ce: "Madina Harami ce tsakanin Dutsen Eir har zuwa Dutsen Sauru, sabda haka duk wanda ya farar da wata Barna a cikinta, ko ya boye wanda ya farar da ita, to La'antar Allah ta tabbata a gare shi da Mala'ikun Allah da Mutane baki daya, Kuma Allah ba zai karbi komai daga gare shi ba na tuba ko kuma na fansa"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

التصنيفات

Hukunce Hukuncen Masallacin Harami da Masallacin Manzon Allah da Baitilmaqdas