Ku Kashe Baqaqe biyu ko a cikin Sallah ne: Macijiya da kuma Kunama

Ku Kashe Baqaqe biyu ko a cikin Sallah ne: Macijiya da kuma Kunama

Daga Anas Dan Malik - Allah ya yarda da shi - ya ce Manon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Ku Kashe Baqaqe biyu ko a cikin Sallah ne: Macijiya da kuma Kunama"

[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi - Al-Darumi Ya Rawaito shi]

الشرح

Wannan Hadisin Maigirma yana bayanin cewa anso a kashe Macijiya da kuma Kunama ko a halin Sallah ne; saboda Umarni da hakan ya zo kuma wancan saboda Motsin kisan takaitacce ne baya vata Sallah

التصنيفات

Sifar Sallah