Sifar Sallah
20- Cewa Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-ya shiga Masallaci,sai wani Mutum ya shigo yayi Salla,sannan yazo yayi sallama ga Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-sai yace:koma kayi Salla,domin cewa kai baka yi Salla ba.sai ya koma yayi Salla kamar yadda yayi Sallar,sannan yazo yayi sallama ga-Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi- sai yace:koma kayi Salla,domin cewa kai bakayi Salla ba-sau Uku-sannan yace:Na rantse da wanda ya aikoka da Gaskiya bazan iya yin wacce tafita ba,to ka sanar dani,sai yace:Idan ka nufi yin Salla kayi Kabbara,sannan ka karanta abinda ya saukaka daga Al-Kur'ani,sannan kayi Ruku'u har sai ka daidaita kana mai Ruku'u,sannan ka dago har ka daidaita kana mai tsayuwa,sannan kayi Sajada har sai ka nutsu kana mai sajada,sannan ka dago har sai ka nutsu kana mai zama.kayi haka acikin kowace Sallarka.