إعدادات العرض
Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku
Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku
Daga usman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi -: Lallai ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai haƙiƙa Shaiɗan ya shiga tsakanina da sallata da kuma karatuna, yana rikitar da ni, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku", sai ya ce: Sai na aikata hakan sai Allah Ya tafiyar da shi daga gareni.
الترجمة
العربية English မြန်မာ Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands اردو Bahasa Indonesia ئۇيغۇرچە বাংলা Türkçe සිංහල हिन्दी Tiếng Việt Kiswahili ไทย پښتو অসমীয়া دری Кыргызча Lietuvių Kinyarwanda नेपाली తెలుగు Bosanski ಕನ್ನಡ Kurdî മലയാളം Oromoo Română Italiano Soomaali Shqip Српски Українська Wolof Moore Tagalog Malagasy தமிழ் Azərbaycan فارسی ქართული 中文 Magyarالشرح
Usman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi - ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah lallai cewa Shaiɗan haƙiƙa ya shiga tsakanina da sallata ya hanani khushu'i a cikinta, ya cakuɗa min karatuna ya sa ni kokwanto a cikinta, Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Wannan Shaiɗan ne ana ce masa Khinzab, idan ka ka sami hakan, kuma ka ji shi ka nemi mafaka a wurin Allah, ka nemi tsarin Allah daga gare Shi, ka yi tofi a hagunka tare da yawu kaɗan sau uku, Usman ya ce: Sai na aikata abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce ni da shi, sai Allah Ya tafiyar da shi daga gareni.فوائد الحديث
Muhimmnacin khushu'i da halartowar zuciya a sallah, kuma cewa Shaiɗan yana ƙoƙari a sa ruɗu da kokwanto a cikinta.
An so neman tsarin Allah daga Shaiɗan a yayin waswasinsa a sallah, tare da tofi a hagu sau uku.
Bayanin abin da sahabbai - Allah Ya yarda da su - suke a kansa na komawarsu zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin abin da yake faruwa garesu na matsaloli har ya warware musu su.
Rayuwar zuciyar sahabbai, kuma cewa himmarsu (damuwarsu) ita ce lahira