Manzon Allah ya kasance in zaiyi salla sai yayi kabbara yayin da yake mikewa, sannan kuma yana yin kabbara yayin da yake yin ruku'u, sannan yana cewa: Allah ya ji mai gode masa, yayin da yake dago bayansa daga raka'a

Manzon Allah ya kasance in zaiyi salla sai yayi kabbara yayin da yake mikewa, sannan kuma yana yin kabbara yayin da yake yin ruku'u, sannan yana cewa: Allah ya ji mai gode masa, yayin da yake dago bayansa daga raka'a

Daga Abu Huraira-Allah ya yarda da shi- yace: Manzon Allah ya kasance in zai yi salla sai ya yi kabbara yayin da yake mikewa , sannan kuma yana yin kabbara yayin da yake yin ruku'u, sannan yana cewa-Allah ya ji mai gode masa, yayin da yake dago bayansa daga raka'a,sannan bayan ya mike yana cewa': ya Ubangijinmu a gare ka dukkanin godiya ta tabbata gare ka, sannan sai ya yi kabbara lokacin da yake tafiya zuwa sujjada, sannan sai ya yi kabbara liokacin sdago kansa daga sujjada, sannansai yayi kabbara yayin da yake yin sujjada, sannan sai yayi kabbara yayinda yake dago kansa, sannan sai ya aikata irin haka a cikin sallarsa dukanta har zuwa karshe, haka kuma yana yin kabbara yayin da yake mike wa daga tahiyar farko, sannan yace: "lallai nine na fiko iya kamant a sallar Manzo tsira da aminci su tabbata a gare shi"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Salla dukkaninta girmama Allah ne ta hanyar zance da aiki, acikin wannan hadisin madaukaki akwai bayanin shiar na salla, shine tabbatar da girma ga Allah madaukaki, babban abin da ya kara nuna girmanta shi ne shar'anta ta da aka yi don girmama Allah da daukaka shi. A lokacin da masallaci zai fara salla sai ya yi kabbarar harama yana tsaye ya daidaita.bayan ya gama karatu ya tafi zuwa ruku'u,sai yayi kabbar, idan ya dago daga ruku'u, sai yace: Allah ya ji mai gode masa ,sai ya mike sosai sai ya godewa Allah ya yabe shi a tsayen,sai ya sake kabbara don kai goshi sujjada, sannan sai ya yi kabbara yayin da yake dago kansa daga sujjada,sai ya aikata haka a cikin dukkan salarsa, har ya kammala,idan ya mike don ciko raka'oi biyu bayan tahiya ta farko sa i ya yi kabbara yayin da yake mikewa. kuma shari'a ta sanya yin kabbara a kowane guri sai dai a waje dagowa daga ruku'u

التصنيفات

Sifar Sallah