Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta

Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta".

[Ingantacce ne] [Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa mafi tsananin mutane muni a sata shi ne wanda yake satar sallarsa; hakan ya kasance ne domin karɓar dukiyar wani wataƙila zai iya amfani da ita a duniya, saɓanin wannan satar, domin ya saci haƙƙin kansa na sakamako da lada, suka ce: Ya Manzon Allah, ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: Ba ya cika ruku'unta kuma ba ya cika sujjadarta; hakan yana nufin ya yi gaggwa a ruku'u da sujjada, ba zai zo da su ba a kan cikkakkiyar fuskar su ba.

فوائد الحديث

Muhimmancin kyautata sallah da zuwa da rukunanta da nutsuwa da ƙanƙar da kai.

Siffanta wanda ba ya cika ruku'unsa da sujjadarsa da cewa shi ɓarawo ne; kyamatar hakan ne gami da faɗakarwa a kan haramcinsa.

Wajabcin cika ruku'u da sujjada a sallah da daidaito a cikinsu.

التصنيفات

Rukunan Sallah, Sifar Sallah, Kusakuren Masu Sallah