Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani

Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani : "(Tsarkakan) Gaisuwa ta tabbata ga Allah, da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne". Acikin wani lafazi na su: "Lallai cewa Allah Shi ne aminci, idan dayanku ya zauna a cikin sallah to ya ce: (Tarakakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agreka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah daalbarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari. Idan ya fadeta za ta samu kowanne bawan Allah nagari a sama da kasa, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ina shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonsa ne, sannan ya zabi abin yake so ya roka".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar da Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - Tahiyar da ake fada a cikin sallah, hakika ya sanya hannunsa a cikin hannayensa, dan ya karkato da hankalin Dan Mas'ud gare shi, kamar yadda yake sanar da shi sura daga Alkur’ani abinda yake nuni akan kulawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wannan Tahiyar lafazi da ma'ana. Sai ya ce: "(Tsarkakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah": Su ne kowacce magana ko aiki mai shirayrwa akan girmamawa, dukkaninsu ababen cancantane ga Allah - Mai girma da daukaka -. "Salloli": Ita ce sananniyar sallah ta farilla da ta nafila, sun tabbata ga Allah - Madaukakin sarki -. "Tsarkakan Maganganu": Su ne maganganu da ayyuka da siffofi tsarkaka masu nuni akan cika, dukkaninsu ababen cancanta ne ga Allah - Madaukakin sarki -. "Aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa': Addu'ace gare shi da aminta daga dukkanin cututtuka da abin ki, da kari da yawaita a kowanne alheri. "Aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari": Addu'ace da aminta daga mai sallah da kuma kowanne bawa na gari a sama da kasa. "Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah': Wato ina tabbatarwa tabbatarwa a yanke cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. "Kuma cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne": Ina tabbatarwa a gare shi da bauta da Manzanci na karshe. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwadaitar da mai yin sallah ya zabi abinda yaso na addu'a ya roka.

فوائد الحديث

Bigiren wannan Tahiyar shi ne zama bayan sujjada ta karshe a kowacce sallah, da kuma bayan raka'a ta biyu a sallah mai raka'a uku da mai raka'a hudu.

Wajabcin gaishe-gaishe a Tahiya, yana halatta ya yi tahiya da kowanne lafazi daga lafazan tahiya daga abinda ya tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Halaccin addu'a da abinda mutum ya so muddin dai ba sabo ba ne.

An so farawa da kai a cikin addu'a.

التصنيفات

Sifar Sallah