Lallai ni wallahi zan yi muku sallah , amma ba sallar nake nufi ba, ina yin sallah ne yadda naga manzon Allah mai tsira da aminchi yake yin sallah.

Lallai ni wallahi zan yi muku sallah , amma ba sallar nake nufi ba, ina yin sallah ne yadda naga manzon Allah mai tsira da aminchi yake yin sallah.

An karbo daga Abi kilabata shi ne Abdullahi dan zaidu aljarmiy albasariy ya ce:{Maaliku dan Huwairisi ya zo wannan masallacin namu, sai ya ce: lallai ni zan yi muku sallah, amma ba sallar nake nufi ba, zanyi sallah kamar yadda naga manzon Allah mai tsira da aminchi su kara tabbata a gareshi yana yin sallah sai na cewa abi kilabata yaya ya kasance yana yin sallah? sai ya ce: kwatankwacin sallar wannan malamin namu, ya kasance yana zama idan ya dago kansa daga sujjada kafin ya mike tsaye} yana nufi da malaminsu Aba buraid, Amru dan salamata aljarmiy

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Abu kilabata yana cewa: Daya daga cikin sahabbai da ake kira maliku dan Huwairis ya zo masallacin mu, sai ya ce: lallai ni na zo wajenku don kawai nayi muku sallah domin na koyar da ku yadda sallar Annabi mai tsira da aminchi su kara tabbata a gareshi take a aikace, don koyarwar ta zamo a surar aiki zaifi zama mafi kusa kuma mafi wanzuwa a cikin kwakwalwar ku. sai marawaicin hadisin ya fada daga Abikilaba: yaya maliku dan Huwairis wannan da ya koyar da ku sallar annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance yana yin sallah? sai ya ce: irin sallar malamin mu Abi yazid shi ne Amru da salamata aljarmiy,ya kasance yana zama sassaukan zama yayi da ya dago kansa daga sujjada don mikewa tsaye, kafin ya tashi tsaye.

التصنيفات

Sifar Sallah