Lallai cewa Ibn umar ya kasance yana sanya Hannayensa kafin guiwoyinsa, kuma ya ce: Manzon Allah SAW ya kasance yana yin hakan

Lallai cewa Ibn umar ya kasance yana sanya Hannayensa kafin guiwoyinsa, kuma ya ce: Manzon Allah SAW ya kasance yana yin hakan

Ibn umar ya kasance yana sanya Hannayensa kafin guiwoyinsa, kuma ya ce: Manzon Allah SAW ya kasance yana yin hakan

[Ingantacce ne] [Ibn Khuzaimah ya rawaito shi]

الشرح

Hadisin yana nuna cewa Mai sallah zai sanya hannayensa kafin Guiwoyinsa lokacin Saunkuyawa domin yin Sujada, sai dai Hadisin Wa'il ya ci karo da shi cewa Mai Sallah lokacin da zai sunkuyo sujada to zai sanya Guiwoyinsa kafin Hannayensa, Kuma Mas'alar ta ijitihadi ce al'amarin yana da yalwa; saboda haka wasu Malamai sin uka bawa Mai Sallah zavin xayan biyun, kodai saboda raunin Hadisan daga vangarorin guda biyu ko kuma saboda cin karonsu da kuma rashin rinjayar da xayana kan xayan a ganinsu, sakamakon hakan aka samu yalwa da kuma zavin duk wanda aka zava cikin biyu

التصنيفات

Sifar Sallah