Ku daidaita a cikin sujjada, kar ku shimfida zira'oinku irin yadda kare ke shimfida nasa.

Ku daidaita a cikin sujjada, kar ku shimfida zira'oinku irin yadda kare ke shimfida nasa.

Daga Anas Dan Malik -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ku daidaita a cikin sujjada, kar ku shimfida zira'oinku irin yadda kare ke shimfida nas

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da aminci yayi umarni da a daidaita cikin sujjada, ta yadda mai yin salla zai kasance cikin kyakkyawar kama a lokacin sujjada, ta yadda zai sa tafukansa a kasa, ya daga zirao'insa ya nesanta su da d kuibukansa, saboda wannan yanayin shi ne alamar karsashi dakwadayi wadanda ake nema a cikin salla, kuma irin wannan yanayin kan bada dama ga ko wace gaba ta sami nata rabon na ibada, an yi hani ga shimfida hannaye a cikin sujjada, don yana jawo lalaci da kosawa, kuma yinsa yin kama da kare ne, wanda bai dace ga mai yin salla ba.

التصنيفات

Sifar Sallah