إعدادات العرض
ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata
ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata
Daga Abu Hazim Dan Dinar Lallai wasu mutane sun zo wa Sahlu ɗan Sa'ad Al-sa'idiy alhali sun yi musu a sha'anin minbarin (Manzon Allah) katakwayensa na mene ne, sai suka tambaye shi game da hakan, sai ya ce: Na rantse da Allah ni na san na mene ne su, haƙiƙa na gan shi a farkon ranar da aka ajiye shi, da kuma farkon ranar da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fara zama a kansa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aika zuwa ga wance - wata mace daga Mutanen Madina -Sahlu ya ambace ta -; "Ki umarci yaronki kafinta ya haɗa min katakwaa da zan zauna a kansu idan zanyiwa mutane magana". Sai ta umarce shi sai ya yisu daga bishiyoyin daji, sannan ya zo da su, sai ta aika zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya yi umarni aka ajiyesu a nan, sannan na ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah a kansu ya yi kabbara alhali yana kansu, sannan ya yi ruku'u alahali yana kansu, sannan ya sauko da baya, sai ya yi sujjada a asalin minbarin sannan ya dawo, yayin da ya gama sai ya fuskanci mutane sai ya ce: "ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata".
الترجمة
العربية English မြန်မာ Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands اردو Bahasa Indonesia ئۇيغۇرچە বাংলা Türkçe සිංහල हिन्दी Tiếng Việt Kiswahili ไทย پښتو অসমীয়া دری Кыргызча Lietuvių Kinyarwanda नेपाली മലയാളം తెలుగు Bosanski Italiano ಕನ್ನಡ Kurdî Oromoo Română Soomaali Shqip Српски Українська Wolof Moore Tagalog O‘zbekالشرح
Wasu mutane sun zo wa ɗaya daga sahabbai suna tambayarsa game da minbarin Annabi wanda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya riƙeshi: Da me aka yi shi? Haƙiƙa sun yi jayayya a hakan, sai ya ambata musu cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aika zuwa ga wata mata daga Mutanen Madina tana da wani yaro kafinta, sai ya ce da ita: Ki umarci yaronki ya yi min minbarin da zan zauna a kansa lokacin da zan yi wa mutane magana, sai matar ta amsa, ta umarci yaronta ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - minbari na bishiyar Ɗarfa'u, lokacin da ya gama sai matar ta aika da munbarin zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya yi umarni da shi sai aka ajiye shi a wurinsa a masallaci, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah a kansa ya yi kabbara alhali yana kansa, sannan ya yi ruku'u alhali yana kansa, sannan ya sauka yana tafiya ta baya, ba tare da ya juyo da fuskarsa ba zuwa ta baya ba, sai ya yi sujjada a asalin minbarin sannan ya dawo, lokacin da ya gama sallar sai ya fuskanci mutane, ya ce: ya ku mutane, kaɗai na aikata haka ne don ku yi koyi kuma ku san sallata.فوائد الحديث
An so riƙon minbari da hawan mai huɗuba a kansa, fa'idarsa ita ce isar wa da kuma jiyarwa.
Halaccin sallah a kan minbari don koyarwa, da halaccin ɗaukakar liman ga mamu don buƙata.
Halaccin neman taimako da masu sana'o'i a buƙatun musulmai.
Halaccin motsi kaɗan a sallah don buƙata.
Halaccin kallon mamu zuwa limaminsa a sallah; don ya koya daga gare shi , kuma hakan ba ya kore khushu'i.
التصنيفات
Sifar Sallah