Na lura da sallar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai na sami tsayuwarsa, da ruku'unsa, da daidaitonsa bayan ruku'u,da sujjadarsa, da zamansa tsakanin sujjada biyu, da zamansa tsakanin sallama da juyawa: kusan daidai da daidai.

Daga Bara'u Dan Azib - Allah ya yarda da shi- yace: "Na lura da sallar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai na sami tsayuwarsa, da ruku'unsa, da daidaitonsa bayan ruku'u,da sujjadarsa, da zamansa tsakanin sujjada biyu, da zamansa tsakanin sallama da juyawa: kusan daidai da daidai

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Bara'u Dan Azib -Allah ya yarda da su- yana sifanta sallar Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi- lokacin da yake lura da sallar Annabi yake kwaikwayonsa, ya ambata mana cewa kusan daidai da daidai ayyukansa suke, saboda tsayuwarsa don karatun salla da zamansa na tahiya kusan daidai suke ga ruku'u da daidaito da sujjada baya dadewa a tsaye kuma yayi gajeren ruku'u, ko ya tsawaita sujjada, sannan kuma ya yi gajeriyar tsayuwa ko zama ba, a'a yana yin ko wane rukuni ya dace da ko wanne. Ba ana nufin : tsayuwa da zaman tahiya su yi daidai da ruku'u ko sujjada ba. Abin nufi ba ya yin wani kadan ya dade a wani.

التصنيفات

Sunnonin Sallah, Sifar Sallah