Naga Manzon Allah SAW yana yiwa Mutane limanci kuma umama Bint Abi Al-as ita ce Xiyar Zainab Xiyar Manzon Allah SAW tana kan kafaxarsa, idan yayi Ruku'u sai ya Ajiye ta, kuma idan ya Xago daga Sujada sai ya Mayar da ita

Daga Abu Qatada Al-ansary -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Naga Manzon Allah SAW yana yiwa Mutane limanci kuma umama Bint Abi Al-as ita ce Xiyar Zainab Xiyar Manzon Allah SAW tana kan kafaxarsa, idan yayi Ruku'u sai ya Ajiye ta, kuma idan ya Xago daga Sujada sai ya Mayar da ita"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Wannan Hadisin Maigirma yana nuna cewa Annabi SAW ya kasance yana Sallah da Mutane kuma a Halim yana xauke da Umama Bint Al-as Xiyar 'Yarsa Zainab -Allah ya yarda da su- har cewa shi yana halin Ruku'u da Sujadarsa idan ya tashi sai ya xauketa haka dai yana nuna cewa babu laifi a cikin xaukar Yara lokacin Sallah

التصنيفات

Sifar Sallah