Manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance yana bude salla da yin kabbara, da karatu, da fadar Alhamdu lillahi rabbil aalamina, ya kasance idan yayi ruku`u baya dago kansa, baya kuma mikar da shi saidai tsaka tsaki

Manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance yana bude salla da yin kabbara, da karatu, da fadar Alhamdu lillahi rabbil aalamina, ya kasance idan yayi ruku`u baya dago kansa, baya kuma mikar da shi saidai tsaka tsaki

An karbo daga A`isha -Allah ya kara yarda a gareta- ta ce: Manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance {yana bude salla da kabbara. da karatu, da fadar Alhamdu lillahi rabbil aalamina, ya kasance idan yayi ruku`u baya dago kansa, ba kuma ya mikar da shi saidai tsaka tsaki, ya kasance idan ya dago kansa daga ruku`i baya yin sujjada, har sai ya daidaita a tsaye, ya kuma kasance idan ya dago kansa daga sujjada, baya kuma sujjada har sai ya daidaita a zaune, ya kasance yana yin tahiya a bayan kowace raka`a biyu, ya kasance yana shimfida kafar sa ta hagu ya kuma kafe kafar sa ta dama, ya kasance yana yin hani gameda irin zaman shaidan. sa`annan yana yin hani mutum ya shimfida hannayen sa guda biyu irin shimfidawar zaki, ya kasance yana rufe sallar da yin sallama}.

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Aisha -Allah ya kara yarda a gareta- tana siffanta sallar annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a garesh i-da wannan hadisin mai girma- saboda yada sunna da isar da wannan ilimi, ya kasance cewa yana bude sallar da kabbarar harama, sai ya ce: (Allahu akbar) yana kuma bude karatu da karatun fatiha, wadda farkon ta tana farawa da (Alhamdu lillahi rabbil aalamin) ya kasance idan yayi ruku`u bayan tsayuwa, baya daga kansa ba kuma ya sunkuyar da shi, kawai dai yana yana sanya shi a mike dai-dai. ya kasance idan ya dago daga ruku`u sai ya kafe a tsaye kafin yayi sujjada ya kasance idan ya dago kansa daga sujjada, baya yin wata sujjadar sai ya dai-daita a zaune ya asance yana fada a bayan kowace raka`a biyu idan ya zauna: ''Attahiyyatu lillahi wassalawatu har zuwa karshe'' ya kasance idan ya zauna sai ya shimfida kafar sa ta hagu sai ya zauna a kanta, ya kuma kafe kafar sa ta dama ya kasance yana hana mai yin salla da ya yi zama a cikin sallar sa irin zaman shaidan, ta yadda zai shimfida kafafuwan sa akan kasa bayan kafafuwan nasa kuma suna kan kasa, ya zauna a karshen dunduniyar sa guda biyu, ko kuma ya kafe kafafuwan sa guda biyu, sa`annan ya sanya mazaunan sa a tsakankanin su akan kasa, kamar yadda yake hana mai yin salla da ya shimfida hannuwan sa guda biyu a cikin sujjada kamar yadda zaki ke shimfida hannuwan sa biyu, kuma kamar yadda ya bude sallar da girmama Allah tare da yin kabbara, yana rufe ta da yin sallama bisa wadanda su ke tare da shi daga mala`iku da masu salla sa`annan bisa dukkan bayin Allah na kwarai, da na farko da na karshe, ya zama wajibi kan mai yin salla da ya lura da wannan gamewa a cikin addu`ar sa.

التصنيفات

Sifar Sallah