Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa:…

Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah

Daga Wa'il ɗan Hujur - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah".

[Hasan ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabin - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin ya juya daga sallarsa zai yi sallama a damansa da hagunsa shi ne ya juyar da fuskarsa ɓangaren dama, tare da faɗinsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), kuma yana yin sallama a hagunsa, shi ne ya juyar da fuskarsa ɓangaren hagu, tare da faɗinsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah).

فوائد الحديث

Halaccin sallama biyu a sallah, kuma ita tana daga rukunanta.

An so zuwa da ƙarin faɗin: (Da albarkarSa), a sashin lokuta; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana dawwama akanta ba.

Furta sallama biyu a cikin sallah rukuni ne na wajibi, amma yin waiwaye a tsakiyar furta su to (Mustahabbi ne) abin so ne.

Yana kamata ya ce: (Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah) a tsakiyar yin waiwaye ba kafinsa ko bayansa ba.

التصنيفات

Sifar Sallah