Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangijina Ka gafarta mini, ya Ubangijina Ka gafarta min'

Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangijina Ka gafarta mini, ya Ubangijina Ka gafarta min'

Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangijina Ka gafarta mini, ya Ubangijina Ka gafarta min'.

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a yayin zama a tsakaknin sujjada biyu: Ya Ubangina ka gafarta min, yana maimaita ta. Ma'anar ya Ubangijina Ka gafarta min: Bawa yana neman daga Ubangijinsa ya shafe masa zunubansa ya suturta aibukansa.

فوائد الحديث

Shar’antuwar wannan addu'ar a tsakanin sujjada biyu a sallar farilla da nafila.

An so maimaita faɗin: Ya Ubangijina Ka gafarta min, wajibi (shi ne) sau ɗaya.

التصنيفات

Sifar Sallah