Lallai cewa Manzon Allah SAW yayi Al-qunuti Wata xaya bayan Ruku'u yana Addu'a ga wasu Mutane daga Qabilar Bani Sulaim

Lallai cewa Manzon Allah SAW yayi Al-qunuti Wata xaya bayan Ruku'u yana Addu'a ga wasu Mutane daga Qabilar Bani Sulaim

Daga Asim ya ce: na tambayi Anas -Allah ya yarda da shi- game da Al-qunuti, ya ce: kafin ya xago daga Ruku'u, sai na ce: lallai cewa Wane yana rayawa cewa kai kana cewa bayan ruku'u? sai ya ce: Yayi qarya, sannan ya gaya mana cewa Manzon Alllah SAW: "cewa shi yayi yayi al-qunuti wata xaya bayan Ruku'u, yana Addu'a ga wasu Mutane daga cikin Bani Sulaim" kuma ya ce: "Ya aika Mutum Arba'in ko Saba'in -yana dai kokwantn yawan- Na Makarantan Qur'ani zuwa ga wasu Mutane Mushirikai" sai waxan can Mutane suka far musu suka kashe su, kuma ya kasance a tsakaninsu akwai Manzon Allah SAW a lokacin "Ban tava ganin sa yayi bacin rai ba kamar bacin rai akan su"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Wanna Hadisin yana bayanin Halaccin Al0qunuti a faruwar Wata Musiba, kuma cewa ita tana kasancewa ne bayan Ruku'u saboda aikin Manzon Allah SAW lokacin da banu sulaim suka warware masa Al-qawarin da ke tsakaninsu da Musulmai da kshe Mutum saba'in ko Arba'in na Makaranta Qur'ani waxan da Manzon Allah SAW ya turasu zuwa gare su sai yayi Al-qunuti wata xaya akan su bayan Ruku'i.

التصنيفات

Sifar Sallah, Nau’o’in Addu’a