Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u sai ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u sai ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa

Daga Ibnu Abi Aufa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u sai ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Allah Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa, cikar sammai da cikar ƙasa da cikar abin da ka so daga wani abu bayan nan"

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u a sallah yana cewa: Allah Ya ji wanda ya gode maSa", wato: Cewa wanda ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki - Allah - Maɗaukakin - sarki Ya amsa masa, Ya karɓi godiyarsa kuma Ya saka masa, sannan ya godewa Allah da faɗinsa; "Ya Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata a greKa, cikon sammai da cikon ƙasa da cikon abin da Ka so daga wani abu bayan nan", godiyar da za ta cika sammai da ƙassai da abin da ke tsakaninsu, kuma ya cika abin da Allah Ya so daga wani abu.

فوائد الحديث

Bayanin abin da ake so masallaci ya faɗe shi idan ya ɗago kansa daga ruku'u.

Halaccin daidaituwa da nutsuwa bayan ɗagowa daga ruku'u; domin cewa ba zai yiwu ba ya faɗi wannan zikirin sai dai idan ya daidaita kuma ya nutsu.

Wannan zikirin abin shara'antawa ne a dukkanin salloli, duk ɗaya ne ta kasance farilla ce ko nafila.

التصنيفات

Sifar Sallah, Zikirin Sallah