Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah,

Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah,

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah, haka nan in zai yi kabbara dan ruku'u, haka idan kuma zai ɗago kansa daga ruku'u sai ya ɗagasu, kuma ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gare ka, ya kasance ba ya yin haka a cikin sujjada.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana ɗaga hannayensa agurare uku a sallah, daura da kafaɗa wanda shi ne: Matattarar ƙashin kafaɗa da damtse. Guri na farko: Idan zai buɗe sallah yayin kabbarar harama. Na biyu: Idan Zai yi kabbara dan ruku'u. Na uku: Idan ya ɗago kansa daga ruku'u kuma ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareka. Ya kasance ba ya ɗaga hannayensa a lokacin fara sujjada, ko lokacin ɗagowa daga sujjada.

فوائد الحديث

Daga hikimomin ɗaga hannaye a cikin sallah cewa hakan ado ne ga sallah da kuma girmama Allah - tsarki ya tabbatar maSa -.

Ɗaga hannaye ya tabbata daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - aguri na huɗu a cikin riwayar Abu Humaid al-Sa'idi a wajen Abu Dawud da waninsa, shi ne lokacin tasowa daga tahiyar farko a sallah mai raka'a uku da mai raka'a huɗu.

Ya tabbata daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi yana ɗaga hannayensa daura da kunnuwansa ba tare da shafa ba, kamar yadda yake a cikin riwayar Malik ɗan Huwairis a cikin Bukhari da Muslim: "Cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi kabbara yana ɗaga hannayensa har sai ya zo dasu daura da kunnuwansa".

Haɗawa tsakanin Tasmi'i da Tahmidi wannan ya keɓanci liman da mai sallah shi kaɗai ne kawai, amma mamu sai ya ce: Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa.

Faɗin: "Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa" bayan ruku'u ne kamar yadda ya inganta daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa akwai sigogi huɗu, wannan ɗaya ce daga cikinsu, abin da yafi nutum ya bibiyi wadannan sigogin ya zo da wannan wani lokaci, wani lokacin kuma da wannan.

التصنيفات

Sifar Sallah