Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta {قل يأيها الكافرون} da {قل هو الله أحد} a raka'o'i biyu (kafin sallar) Asuba

Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta {قل يأيها الكافرون} da {قل هو الله أحد} a raka'o'i biyu (kafin sallar) Asuba

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta {قل يأيها الكافرون} da {قل هو الله أحد} a raka'o'i biyu (kafin sallar) Asuba.

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son a raka'o'i biyu na nafilar Asuba, a raka'a ta farko ya karanta surar {قل يأيها الكافرون} [al-Kafirun]. A raka'a ta biyu kuma surar {قل هو الله أحد} [al-Ikhlas].

فوائد الحديث

An so karanta waɗannan surori biyun bayan fatiha a sunnar (Raka’atal fajr) Asuba.

Waɗannan surori biyun ana ce musu Suratul Ikhlas; domin a cikin Suratul kafirun akwai kuɓuta daga dukkan abinda mushrikai suke bautawa koma bayan Allah, kuma su ba masu bautar Allah ba ne domin shirkarsu tana ɓata ayyukansu, kuma Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne Mai wanda ya cancanci ibada, kuma cewa a cikin Suratul al-Ikhlas akwai kaɗaita Allah (da bauta) da kuma tsarkake (ibada) gare shi da bayanin siffofinSa.

التصنيفات

Sifar Sallah