Naga Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yanazaune ya tanqwashe Qafafunsa

Naga Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yanazaune ya tanqwashe Qafafunsa

Da Hadisin Aisha Allah ya yarda da ita ta ce: Naga Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yanazaune ya tanqwashe Qafafunsa

[Ingantacce ne] [Al-Nasa'i Ya Rawaito shi]

الشرح

Tarabbu'e: Zhi ne ya sanya cikin tafin kafarsa a qarqashin cinyarsa ta Hagu, kuma cikin Hagunsa a qarqashin cinyar Dama, kuma ya zauna akan Mazaunansa, kuma haqiqa Manzon Allah SAW wannan yayin da ya faxo ne daga kan Dokinsa, kuma kuma yayi targaxe a Qafarsa, to idan mai sallah ya gajiya ga barin tsayuwa to yayi Sallah a zaune Mustahabi ne, kuma wannan a cikin Halin zamansa a maimakon tsayuwa, amma a lokacin zamansa a tsakani Sujadodi guda biyu, da zamansa a tsakani tahiya guda biyu, da zamansa a tsakanin tahiyoyi guda biyu, to an so ya zauna yana Mai zaman Iftirash a tahiyar farko, da kuma zaman Tawarruk a tahiya ta Biyu, kuma dukkan waxan nan Siffofin suna daga cikin babin Mustahabanci da kuma fifiko, da ace zai sava kuma ya zauna akan wata kamar ba wannan ba to da ya isar masa; saboda abun nema shi ne zaman domin Tahiyar kuma waxan Siffofi gwargwado ne na Wajibi

التصنيفات

Sallar Masu Uzuri