إعدادات العرض
Manzon Allah SAW yayi Maka Istigfari? ya ce: Ey, haka ma kai sannan ya karanta wannan Ayar: "Kuma ka nemi gafarar zunubanka da kuma Muminai Maza da Mata"
Manzon Allah SAW yayi Maka Istigfari? ya ce: Ey, haka ma kai sannan ya karanta wannan Ayar: "Kuma ka nemi gafarar zunubanka da kuma Muminai Maza da Mata"
Daga Abdullahi Bn Sarjis, ya ce: naga Manzon Allah SAW kuma muka ci Gurasa da Nama tare da shi, ko kuma ya ce: Tharid, ya ce: sai na ce da shi: Manzon Allah SAW yayi Maka Istigfari? ya ce: Ey, haka ma kai sannan ya karanta wannan Ayar: "Kuma ka nemi gafarar zunubanka da kuma Muminai Maza da Mata" [Muhammad" ya ce: sannan na kewa bayansa sai naga Hatimin Annabta a tsakanin Kafaxunsa, a gefen Kafaxarsa na Hagu, kamar dunqulen hannu, akansa tabo, Kamar qwan tattabara
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]
الشرح
Babban Sahabin Annabi Abdullahi Bn Sarjis yana cewa: cewa shi yaga Manzon Allah SAW kuma muka ci Gurasa da Nama tare da shi, ko kuma ya ce: Tharid, ya ce: sai na ce da shi: Manzon Allah SAW yayi Maka Istigfari? ya ce: Ey, haka ma kai sannan ya karanta wannan Ayar: "Kuma ka nemi gafarar zunubanka da kuma Muminai Maza da Mata" [Muhammad19: " ya ce: sannan na kewa bayansa sai naga Hatimin Annabta a tsakanin Kafaxunsa, a gefen Kafaxarsa na Hagu, kamar dunqulen hannu, akansa tabo, Kamar qwan tattabara, kuma ya sava da launin jikinsa SAW, kuma wannan baya savawa da riwayar da ta sifanta Hatimin da gashi ne da ya tattaru wuri xaya, da kuma wanda ya Kamanta ta Qwan Tattabara, to dukkan waxan can zai yiwu su taru wuri xaya.التصنيفات
Abubuwan da Annabi ya kevanta da su