Bana kishin Mutuwar wani da Mutuwa da tafi bani tsoro da tsanani kamar Mutuwar Manzon Allah SAW

Bana kishin Mutuwar wani da Mutuwa da tafi bani tsoro da tsanani kamar Mutuwar Manzon Allah SAW

Daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita ta ce: "Bana kishin Mutuwar wani da Mutuwa da tafi bani tsoro da tsanani kamar Mutuwar Manzon Allah SAW"

[Ingantacce ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

Nana Aisha tana cewa: lallai cewa ita ba zatayi farin ciki da sauqin Mutuwar wani ba, kuma ba zata yi fatan ta zama mai sauqi ba, bayan abun da ta gani ga Manzon Allah SAW haqiqa tasan cewa tsananin Mutuwa ba ita ce take nuna Mummunan qarshe ga mamaci ba, kuma ba saqinta ba ne yake nuna Karama ba, kuma inda haka ne da Manzon Allah SAW ya kasance Mafi cancantar Mutane da shi, to don haka kada kuji tsoron tsananin Mutuwa, kuma kada kuyi farin cikin don wani ya Mutu ba tare da tsanani ba.

التصنيفات

Wafatinsa SAW