Lallai ba'a karvar ran wani Annabi face sai an nuna masa Masaukinsa a Al-janna, sannan a bashi zavi" to yayin da Mutuwa ta sauka gare shi, Kansa yana kan cinyata sai ya suma, sannan ya farka sai idonsa ya kafe yana kallon rufin xakin, sannan ya ce: "Ya Ubangiji kusanci Mafi xaukaka"

Lallai ba'a karvar ran wani Annabi face sai an nuna masa Masaukinsa a Al-janna, sannan a bashi zavi" to yayin da Mutuwa ta sauka gare shi, Kansa yana kan cinyata sai ya suma, sannan ya farka sai idonsa ya kafe yana kallon rufin xakin, sannan ya ce: "Ya Ubangiji kusanci Mafi xaukaka"

An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce: Manzon Allah SAw ya kasance yana cewa a halin yana cikin lafiyarsa: "Lallai ba'a karvar ran wani Annabi face sai an nuna masa Masaukinsa a Al-janna, sannan a bashi zavi" to yayin da Mutuwa ta sauka gare shi, Kansa yana kan cinyata sai ya suma, sannan ya farka sai idonsa ya kafe yana kallon rufin xakin, sannan ya ce: "Ya Ubangiji kusanci Mafi xaukaka"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- tana cewa: Manzon Allah ya kasance a lokacin yanada lafiya yana cewa kafin yayi rashin lafiyar Mutuwarsa: cewa babu wani Annabi da zai Mutu daga cikin Annabawa har sai Allah ya nuna masa Mahallinsa a Aljanna, sannan ya bashi zavin zama a Duniya ko kuma ya xaukeshi zuwa Masaukinsa a Aljanna, Aisha ta ce: yayin da manzon Allah SAW yayi rashin lafiyar Mutuwarsa, kansa yana kan cinya ta, sai ya suma sannan ya farka, sai ya xaga kansa zuwa rufin xakin sannan ya ce: "Ya Ubangiji zuwa Makwabtaka Maxaukakiya" ai ya zavi kusanci su ne Jama'ar Annabawa waxanda suke zaune a sama sama, Nana Aisha ta ce idan Allah ya bashi zavin tsakanin Duniya da Lahira to shi zai zavi Lahira ne, ba zai zave mu ba, kuma nasan cewa wannan zavin shi ne zancen da yake gaya mana lokacin yana lafiya, Aisha ta ce: Qarshen kalmar da ya faxa SAW ita ce: "Ya Ubangiji zuwa Makwabtaka Maxaukakiya"

التصنيفات

Wafatinsa SAW