Wata rana Manzon Allah SAW ya futo da Hasan, sai ya hau kan Minbari, sai ya ce: Wannan Xana ne Kuma Shugaba, kuma watakila Allah zai sulhunta tsakanin wata runduna guda biyu ta Musulmai

Wata rana Manzon Allah SAW ya futo da Hasan, sai ya hau kan Minbari, sai ya ce: Wannan Xana ne Kuma Shugaba, kuma watakila Allah zai sulhunta tsakanin wata runduna guda biyu ta Musulmai

Daga Abu Bakra -Allah ya yarda da shi- ya ce: Wata rana Manzon Allah SAW ya futo da Hasan, sai ya hau kan Minbari, sai ya ce: Wannan Xana ne Kuma Shugaba, kuma watakila Allah zai sulhunta tsakanin wata runduna guda biyu ta Musulmai

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Wata rana Manzon Allah SAW ya futo da Hasan, zuwa Masallaci sai ya hau kan Minbari, sai ya ce: Wannan Xana ne Kuma Shugaba, Sai ya bawa Muatane labari cewa Xansa Hassan Shugaba ne Mai Asalin girma, Kuma Mai darajar Nasaba, kuma yana dangantaka da mafi girman gida a bayan qasa, kuma cewa Allah Maxaukakin Sarkin kuma watakila Allah zai sulhunta tsakanin wata runduna guda biyu ta Musulmai ya haxa kan baki xayan Musulmai, Kuma babu Shakka wannan hadisin mai girma Alama daga cikin Alamomin Annabtakarsa SAW inda a cikin wannan Hadisin yanda ya bada labarin sa SAW abunda zai faru ga wannan jagora ne mai girma Alhasan Bin Ali -Allah ya yarda da su- na haca kan Musulmai da sulhu a tsakaninsu, da xauke rigimar tsakaninsu, kuma hakan ya faru ta hanyar janyewarsa daga Halifanci ga Mu'awiya, abunda xinkewar varaka, da kuma kate jini kuma wana ya faru ne a Shekarar Jama'a Shekara ta 40 ko 41 hijira

التصنيفات

Falalar Ahlul Baiti