إعدادات العرض
1- Alhasan da Alhusain su ne shugabannin matasan 'yan Aljanna
2- Wata rana Manzon Allah SAW ya futo da Hasan, sai ya hau kan Minbari, sai ya ce: Wannan Xana ne Kuma Shugaba, kuma watakila Allah zai sulhunta tsakanin wata runduna guda biyu ta Musulmai
3- Ban kasance mai kishin daya daga cikin matan Annabi ba - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba na kishin Khadija - Allah Ya yarda da ita - kuma ban taba ganinta ba, amma ana yawan ambatonta.
4- Ku kalli wannan yana tambaya ta game da jinin Sauro, Kuma haqiqa ankashe Xan Manzon Allah SAW kuma naji Manzon Allah SAW yana cewa: suna daxin Qanshi na na Duniya
5- Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi, sai ya faɗi abinda Allah Ya umarce shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai cewa mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], ya Allah Ka bani lada a cikin wannan musibar tawa kuma Ka musanya mini da mafi alheri da ita, sai Allah Ya musanya masa da mafi alheri daga ita
6- Yayin da Ibarahim ya Mutu Manzon Allah SAW ya ce: "Lallai yana da Mai shayar da shi a cikin Al-janna"