إعدادات العرض
: :
: :
Daga Ummu Salamah Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi, sai ya faɗi abinda Allah Ya umarce shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai cewa mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], ya Allah Ka bani lada a cikin wannan musibar tawa kuma Ka musanya mini da mafi alheri da ita, sai Allah Ya musanya masa da mafi alheri daga ita", ta ce: Lokacin da Abu Salama ya rasu na ce: Waye a cikin musulmai ya fi Abu Salama alheri? farkon gidan da ya yi hijra zuwa ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan sai na faɗeta (addu'ar), sai Allah Ya maye mini gurbinsa da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
الترجمة
العربية Tiếng Việt Bahasa Indonesia Nederlands Kiswahili অসমীয়া English ગુજરાતી සිංහල Magyar ქართული Română ไทย Portuguêsالشرح
Uwar muminai Ummu Salama - Allah Ya yarda da ita - ta ambaci cewa ita ta ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa wata rana: Babu wani musulmin da wata musiba zata same shi sai ya faɗi abinda Allah Ya so gare shi: {Lallai mu daga Allah muke kuma lallai mu zuwa ga Allah zamu koma} [al-Baƙara: 156], (Ya Allah Ka bani lada) Ka bani ladan haƙurina (a cikin wannan musiba), ka canja mini (Ka maye mini gurbi) daga ita (da mafi alheri daga gareta); sai Allah Ya canja masa mafi alheri daga gareta. Ta ce : Lokacin da Abu Salama ya yasu na ce: Waye cikin musulmai ya fi Abu Salama alheri?! farkon gidan da ya yi hijira zuwa ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan Allah Ya taimake ni sai na faɗeta, sai Allah Ya maye mini gurbin Abu Salama da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbta agare shi -.فوائد الحديث
Umarni da haƙuri a lokacin musibu da kuma rashin kururuwa.
Fuskantar da addu'a zuwa ga Allah a cikin musibu da suke sauka; domin canji yana gare shi (shi Allah).
Larurar mumini ya yi ruko da umarnin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - koda hikima bata bayyana daga umarninsa ba.
Alheri dukkansa yana cikin ruko da umarnin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.