"Ya ke Aish, Wannan Jibril ne yana gaisheka" Sai na ce: Amincin Allah da rahamarsa su tabbara a gareshi, kana ganin abinda bana gani

"Ya ke Aish, Wannan Jibril ne yana gaisheka" Sai na ce: Amincin Allah da rahamarsa su tabbara a gareshi, kana ganin abinda bana gani

An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce: Wata Rana Manzon Allah ya ce: "Ya ke Aish, Wannan Jibril ne yana gaisheka" Sai na ce: Amincin Allah da rahamarsa su tabbara a gareshi, kana ganin abinda bana gani.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Manzon Allah SAW ya bawa Aisha labarin cewa Mala'ika Jibril yana gaida ta sai ta ce: Amincin Allah a gareshi da rahamarsa da Albakatansa, Lallai kai Manzon Allah SAW kana ganin abunda bana gani, tana nufin cewa Manzon Allah SAW ya ganin Mala'ika Jibril wanda kuma ita bata ganinsa

التصنيفات

Falalar Iyayen Muminai (Matan Annabi), Matansa SAW da halin gidan Annabta