Mutane da yawa su cika Mutane, amma daga cikin Mata babu waxanda suka cika sai Asiya Matar fir'auna, da Maryam Bint Imran, kuma lallai cewa Falalar Aisha akan sauran Mata kamar Falalar Al-tharid kan sauran abinci

Mutane da yawa su cika Mutane, amma daga cikin Mata babu waxanda suka cika sai Asiya Matar fir'auna, da Maryam Bint Imran, kuma lallai cewa Falalar Aisha akan sauran Mata kamar Falalar Al-tharid kan sauran abinci

An karvo daga Abu Musa -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Mutane da yawa su cika Mutane, amma daga cikin Mata babu waxanda suka cika sai Asiya Matar fir'auna, da Maryam Bint Imran, kuma lallai cewa Falalar Aisha akan sauran Mata kamar Falalar Al-tharid kan sauran abinci"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Lallai waxanda suka kai Matsayin cika a cikin Falalar Addini da Halayya daga cikin Maza akwai da yawa daga cikinsu akwai wanda yakai Matakin cika ta Al-ada Kamar Malamai da Mutanen kirki da Waliyyai, akwai daga cikin su akwai wanda ya wuce matakin cika kamar Annabwa, amma Matan da suka cika su ne kaxan kwarai kuma waxanda suke gaba Asiya Matar Fir'auna ita Asiya Bint Muzahim wacce Allah ya buga Misali da ita a cikin cikar Imani, sai ya ce: "Kuma Allah ya buga Misali ga waxanda sukai Imani Matar fir'auna" Saboda tayi Imani da Annabi Musa lokacin da yai Nasara kan Masu Sihirin fir'auna, kuma yayin da fir'auna ya san ta yi Imani sai yayi mata Azaba Mai tsanani har zuwa lokacin da ta Mutu tana riqe da Imaninta, amma ta biyu ita ce Maryam Bint Imran wacce Allah ya buga Misali wajen kare kanta, da kuma cikar Ibadarta, sannan SAW ya ce: "Kuma falalar Aisha kan sauran Mata kamar fifikon Tharid kan sauran Abinci" Tharid shi ne mafi daxin abincin Larabawa kuma anayinsa ne da gurasa da kuma nama, to Aisha a Fifikon ta kan Mata kamar Fifikon wancan Tharid xin wanda shi ne mafi daxin abinci kan Sauran Abinci

التصنيفات

Falalar Iyayen Muminai (Matan Annabi), Matansa SAW da halin gidan Annabta