Ban taba ganin wani mutum da ya Manzon Allah SAW ya fansheshi ba bayan Sa'ad naji shi yana cewa: Ka harba fansarka da Mahaifana

Ban taba ganin wani mutum da ya Manzon Allah SAW ya fansheshi ba bayan Sa'ad naji shi yana cewa: Ka harba fansarka da Mahaifana

Daga Ali -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Ban taba ganin wani mutum da ya Manzon Allah SAW ya fansheshi ba bayan Sa'ad naji shi yana cewa: Ka harba fansarka da Mahaifana"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Ali -Allah ya yarda da shi- yana bada labari cewa shi bai tava ganin Manzon Allah SAW yana fansar wani Mutum ba bauan Sa'ad Bn Abi Waqqae -Allah ya yarda da shi- lokacin da Manzon Allah SAW yaji shi yana cewa da shi a lokacin Yaqin Uhud, ka jefi kafirai da Mashi ina fansarka da Mahaifana, ai ina gabatar da Mahaifana don su zamo fansa a gareka kai ka tsira, kuma ya tabbata a cikin Ingantaccen hadisi cewa Manzon Allah SAW ya fanshi Zubai -Allah ya yarda da shi- da Iyayensa a Yaqin Khandaq, Kuma ana iya haxa tsakaninsu da cewa Ali -Allah ya yarda da shi- bai san hakan ba, ko kuma nufinsa yana taqaicewa ne kawai a Yaqin Uhud

التصنيفات

Falalar Sahabbai -Amincin Allah a gare su-