Sunyi Gaskiya, lallai su ana yi musu Azaba Azabar da Dabbobi suke ji baki xayansu

Sunyi Gaskiya, lallai su ana yi musu Azaba Azabar da Dabbobi suke ji baki xayansu

An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- ta ce: Wasu tsoffin Mata guda biyu daga cikin tsoffin Yahudawan Madina sun shigo mun, sai suka ce da ni: Lallai Na Qabari ana yi musu Azaba a cikin Qabarinsu, sai na qaryatasu, kuma ban so na gasgata su ba, sai suka futa, kuma Manzon Allah SAW ya shigo sai na ce da shi: ya Manzon Allah, Wasu tsoffin Mata biyu kuma na gaya masa labarin, sai ya ce:"Sunyi Gaskiya, lallai su ana yi musu Azaba Azabar da Dabbobi suke ji baki xayansu" kuma ban tava ganinsa a wata sallah ba face sai ya nemi tsari daga Azabar Qabarin

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Wasu tsoffin Mata guda biyu daga cikin tsoffin Yahudawan Madina sun shigo mun, sai suka ce da ni:Lallai Na Qabari ana yi musu Azaba a cikin Qabarinsu, sai na qaryatasu, kuma ban so na gasgata su ba, sai suka futa, kuma Manzon Allah SAW ya shigo sai na ce da shi: ya Manzon Allah, Wasu tsoffin Mata biyu kuma na gaya masa labarin, sai ya ce:"Sunyi Gaskiya, lallai su ana yi musu Azaba Azabar da Dabbobi suke ji baki xayansu" kuma ban tava ganinsa a wat a sallah ba face sai ya nemi tsari daga Azabar Qabarin

التصنيفات

Rayuwar Barzahu, Zikirin Sallah, Addu’o’I da aka samu daga Annabi