إعدادات العرض
1- Ku saurara, kada wani mutum Hadisi ya je masa daga gareni alhali shi yana kishingide akan mazauninsa sai ya ce: Tsakanin mu da ku littafin Allah
2- Annabi tsir da aminci Allah ya wuce wasu kabarurruka biyu, sai yace: lallai ana yi musu azaba, ba don wani babban laifi ake musu azaba ba, dayansu yakasance baya buya idan zai yi fitsari, kuma baya yin yadda zai kare kansa daga yadda fitsarin zai iya fallarsar masa,dayan kuma ya kasance mai yada annamimanci.
3- Idan aka nemi Musulmi a cikin kabari ya ba da shaidar cewa babu wani abin bauta sai Allah, kuma Muhammadu Manzon Allah ne, to wannan shi ne abin da Madaukaki ya ce: Allah Yana tabbatar da wadanda suka yi imani da magana tabbatacciya a rayuwa da duniya
4- Sunyi Gaskiya, lallai su ana yi musu Azaba Azabar da Dabbobi suke ji baki xayansu
5- Lallai daga cikin alamomin tashin Alkiyama, za’a dauke ilimi, jahilci zai yi yawa, zina zata yawaita, za’a yawaita shan giya, maza za su yi karanci, mata za su yi yawa, har sai ya kasance mata hamsin mutum daya ne yake kula da su
6- Alkiyama ba za ta tsaya ba har sai mutum ya wuce wani kabari sai ya ce: Ina ma dai ni ne a wurin nan
7- Alkiyama ba zata ta shi ba har sai kun yaki Yahudawa, har sai dutsen da a bayansa akwai bayahude ya ce: Ya kai Musulmi, wannan bayahude ne ka kashe shi
8- Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, Ibnu Maryam (Annabi Isa) ya kusa ya sauka a cikinku yana mai hukunci mai adalci, sai ya karya gicciyayye (cross), ya kashe alade, ya sarayar da jizya, dukiya ta yawaita har babu wanda zai karbeta
9- Alkiyama ba zata tashi ba har sai rana ta bullo ta mafadarta, idan ta bullo mutane suka ganta sai su yi imani gaba dayansu
10- Alkiyama ba zata tsaya ba har sai zamani ya kusantowa juna
11- Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci wani abu, sai ya ce: "Wannan a lokacin tafiyar ilimi kenan
12- Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su
13- Idan ya yi kyau, sai ta ce: Ka zo da ni, ka kawo ni gabana, idan kuma bai inganta ba, sai ta ce: Kaitona! Ina zaka tafi dashi
14- Tsakanin ffsan fuka fukai arba'in, suka ce: Ya Abu Huraira kwana arba'in? Ya ce: Shin kun ƙi? Sai suka ce: Shekara arba'in? Ya ce: Na ki. Suka ce: Watan arba'in? Ya ce: Na ki
15- Haqiqa anyi mun Wahayi cewa ku za'a Jarrabeku a cikin Qabarinku kusan Fitinar Dujal