Alkiyama ba zata ta shi ba har sai kun yaki Yahudawa, har sai dutsen da a bayansa akwai bayahude ya ce: Ya kai Musulmi, wannan bayahude ne ka kashe shi

Alkiyama ba zata ta shi ba har sai kun yaki Yahudawa, har sai dutsen da a bayansa akwai bayahude ya ce: Ya kai Musulmi, wannan bayahude ne ka kashe shi

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Alkiyama ba zata ta shi ba har sai kun yaki Yahudawa, har sai dutsen da a bayansa akwai bayahude ya ce: Ya kai Musulmi, wannan bayahude ne ka kashe shi".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Alkiyama ba zata tsayaba har sai musulmi da yahudawa sun yi yaki, Har idan bayahude ya gudu bayan dutse dan ya buyarwa musulmi; Allah zai sa dutsen ya yi magana ya kira musulmin: Da cewa akwai bayahude a bayansa har ya zo dan kashe shi.

فوائد الحديث

Bada labarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wasu daga abubuwan dake boye da masu zuwa, yayin da Allah - Madaukakin sarki - Ya tsinkayar da shi, to shi zai afku babu makawa.

Yaki tsakanin musulmai da yahudawa a karshen zamani, kuma wannan yana daga alamomin Alkiyama.

Wanzuwar addinin Musulunci har zuwa ranar Alkiyama, da nasararsa akan addinai gaba daya.

Taimakon Allah ga musulmai akan makiyansu, daga wannan akwai sanya dutse ya yi magana a karshen zamani.

التصنيفات

Rayuwar Barzahu