Alkiyama ba zata tsaya ba har sai zamani ya kusantowa juna

Alkiyama ba zata tsaya ba har sai zamani ya kusantowa juna

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Alkiyama ba zata tsaya ba har sai zamani ya kusantowa juna, sai shekara ta zama kamar wata, wata kuma ya zama kamar Juma'a (sati guda), Juma'a kuma ta zama kamar yini, yini ya zama kamar awa, awa kuma ta zama kamar konewar ganyen dabino".

[Ingantacce ne] [Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bada labarin cewa daga alamomin Alkiyama akwai kusantowar zamani, sai shekara ta wuce kamar yadda wata yake wucewa, wata kuma ya wuce kamar yadda sati yake wucewa, Juma'a (sati) ya wuce kamar yadda yini yake wucewa, yini ya wuce kamar yadda awa daya take wucewa, awa ta wuce da gaggawa mai tsanani kamar yadda ganyan bishiyar dabino yake konewa.

فوائد الحديث

Daga alamomin Alkiyama cire albarka a zamani ko gaggawarsa.

التصنيفات

Rayuwar Barzahu