Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su

Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su

Daga Abu Huraira daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - lallai ya ce: "Za a samu wasu mutane a ƙarshen al'ummata suna zantar da ku abin da ku da iyayenku ba ku ji ba, to, kashedinku da su"

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wasu mutane a ƙarshen al'ummata za su bayyana suna ƙirƙirar ƙarya, kuma suna faɗin abin da wani kafinsu bai faɗa ba, suna ba da labarai da hadisan ƙarya abubuwan ƙirƙira, sai (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gareshi ya umarcemu mu nisancesu kada mu zauna da su, kuma kada mu ji hadisansu; don kada ƙirƙirarran hadisin ya tabbata a cikin zukata, sai mu kasa kuɓuta daga su.

فوائد الحديث

A cikinsa akwai alama daga alamonin Annabta, yayin da Annabi - tsira da aminin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labain abin da zai afku a cikin al'ummarsa, sai ya afku kamar yadda ya ba da labari.

Nisantar wanda zai yi ƙarya ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - haka kuma [da yin ta] ga Addinin Musulunci, da [buƙatar] kada a saurari ƙaryarsu.

Gargaɗi game da karɓar Hadisai ko yaɗa su sai bayan tabbatarwa game da ingancinsu da tabbatarsu.

التصنيفات

Muhimmancin Sunna da Matsayinta, Rubuta Sunnar Annabi, Rayuwar Barzahu