Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad manzon Allah ne

Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad manzon Allah ne

Daga Bara'u ɗan Azib - Allah Ya yarda da shi - manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad manzon Allah ne". to wannan shi ne faɗinSa: {Allah Yana tabbatar wa waɗanda suka yi imani da faɗa tabbatacciya a cikin rayuwar duniya da kuma lahira} [Ibrahim: 27].

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Za'a tambayi mumini a cikin ƙabari, sai mala'iku biyu waɗanda aka wakilta da hakan su tambaye shi su ne Munkar da Nakir, kamar yadda ambatansu ya zo a Hadisai masu yawa, sai ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: wannan shi ne tabbatacciyar magana wacce Allah Ya faɗa a cikinta: {Allah Yana tabbatar da wadanda su ka yi imani da magana matabbaciya a rayuwar duniya da kuma a lahira} [Ibrahim: 27].

فوائد الحديث

Lallai cewa tambayar ƙabari gaskiya ne.

Falalar Allah ga bayinSa muminai a duniya da lahira ta hanyar tabbatar da su akan tabbatacciyar magana.

Falalar shaidawa da Tauhidi da mutuwa akan hakan.

Tabbatar war Allah ga mumini a duniya da tabbata akan imani, da shiga hanya madaidaiciya, a lokacin mutuwa kuma da mutuwa akan Tauhidi, a ƙabari a lokacin tambayar mala'iku biyu.

التصنيفات

Rayuwar Barzahu