Lallai daga cikin alamomin tashin Alkiyama, za’a dauke ilimi, jahilci zai yi yawa, zina zata yawaita, za’a yawaita shan giya, maza za su yi karanci, mata za su yi yawa, har sai ya kasance mata hamsin mutum daya ne yake kula da su

Lallai daga cikin alamomin tashin Alkiyama, za’a dauke ilimi, jahilci zai yi yawa, zina zata yawaita, za’a yawaita shan giya, maza za su yi karanci, mata za su yi yawa, har sai ya kasance mata hamsin mutum daya ne yake kula da su

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wallahi zan zantar daku wani hadisin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wanina ba zai zantar daku shi ba: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Lallai daga cikin alamomin tashin Alkiyama, za’a dauke ilimi, jahilci zai yi yawa, zina zata yawaita, za’a yawaita shan giya, maza za su yi karanci, mata za su yi yawa, har sai ya kasance mata hamsin mutum daya ne yake kula da su".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa daga alamomin kusantowar tashin Alkiyama dauke ilimi na shari'a, wannan kuwa ta hanyar mutuwar malamai ne. Sakamakon hakan jahilci zai yawaita ya yadu, zina da alfasha zasu yadu, shan giya zai yawaita, adadin maza zai karanta , adadin mata zai karu; har yakasance namiji daya zai tsayawa mata hamsin ga al'amuransu kuma zai jibinci maslahohinsu.

فوائد الحديث

Bayanin wasu daga cikin alamomin Alkiyama.

Sanin lokacin Alkiyama yana daga al'amuran gaibu wadanda Allah ne kadai ya san su.

Kwadaitarwa akan neman ilimin shari'a kafin a rasa shi..

التصنيفات

Rayuwar Barzahu, Falalar Ilimi