Alkiyama ba za ta tsaya ba har sai mutum ya wuce wani kabari sai ya ce: Ina ma dai ni ne a wurin nan

Alkiyama ba za ta tsaya ba har sai mutum ya wuce wani kabari sai ya ce: Ina ma dai ni ne a wurin nan

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Alkiyama ba za ta tsaya ba har sai mutum ya wuce wani kabari sai ya ce: Ina ma dai ni ne a wurin nan".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bada labarin cewa Alkiyama ba za ta tsaya ba har sai mutum ya wuce kabari, sai ya yi burin ya zama matacce a bigirensa, sababi shi ne tsoronsa akan kansa na tafiyar Addininsa saboda rinjayar karya da ma'abotanta, da bayyanar fitintinu da sabo da abubuwan ki.

فوائد الحديث

Nuni da bayyanar sabo da fitintinu a karshen zamani.

Kwadaitarwa akan riko da kiyayewa da yi wa mutuwa tanadi ta hanyar yin imani da ayyuka na gari, da nisanta daga guraren fitintinu da bala'o'i.

التصنيفات

Rayuwar Barzahu, Halayen Mutane na Qwarai, Tsarkake Zuciyoyi