Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci

Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci

Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu, sai ya ce: "Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci" Sannan ya dauki wani danyan itacan dabino, sai ya raba shi biyu, sai ya kafa daya a kowanne kabari, suka ce: Ya Manzon Allah, meyasa ka aikata hakan, sai ya ce: "Watakila a saukaka musu muddin dai basu bushe ba".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu sai ya ce: Lallai masu kaburburan nan biyu ana musu azaba; kuma ba'a yi musu azaba dan wani babban laifi ku a ganinku ba, duk da yake mai girma ne a wurin Allah, amma dayansu ya kasance ba ya himmantuwa da kiyaye jikinsa da tufafinsa daga fitsari har sai ya biya bukatarsa, dayan kuma ya kasance yana tafiya da annamimanci a tsakanin mutane, sai ya dakko zancen wani da nufin cutarwa da sanya sabani da fitina a tsakanin mutane.

فوائد الحديث

annamimanci da barin tsarkaka daga fitsari yana daga manyan zunubai kuma daga sabubban azabar kabari.

Allah - tsarki ya tabbatar maSa - ya yaye wasu sashin gaibu - kamar azabar kabari - dan bayyanar da alamar Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Wannan aikin na tsaga itacan dabino da sanya shi akan kabari ya kebanci Annabi ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ; domin Allah Ya tsinkayar da shi akan halin masu kabarin su biyun, ba za’a kiyasta waninsa da shi ba domin babu wani da yasan halayen ma'abota kaburbura.

التصنيفات

Rayuwar Barzahu, Rayuwar Barzahu, Munanan Halaye, Munanan Halaye, Abubuwan tsoron cikin Qabari, Abubuwan tsoron cikin Qabari