Ku saurara, kada wani mutum Hadisi ya je masa daga gareni alhali shi yana kishingide akan mazauninsa sai ya ce: Tsakanin mu da ku littafin Allah

Ku saurara, kada wani mutum Hadisi ya je masa daga gareni alhali shi yana kishingide akan mazauninsa sai ya ce: Tsakanin mu da ku littafin Allah

Daga Mikdam dan Maadikarib - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbata agare shi - ya ce "Ku saurara, kada wani mutum Hadisi ya je masa daga gareni alhali shi yana kishingide akan mazauninsa sai ya ce: Tsakanin mu da ku littafin Allah, abinda muka samu na halal a cikinsa mu halattashi, abinda muka samu a cikinsa na haram mu haramtashi, kuma lallai abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haramta to kamar abinda Allah Ya haramtane".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bada labarin cewa hakika wani lokaci ya kusa , wani sinfi na mutane zasu zamo acikinsa a zaune, dayansu yana kishingide akan shinfidarsa, Hadisi zai isar masa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Abinda zai raba tsakaninmu da ku a cikin al'amura shi ne Alkur’ani Mai girma shi ya ishemu, abinda muka samu a cikinsa na halal mu yi aiki da shi, abinda muka samu a cikinsa na haram mu nisance shi. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa duk abinda ya haramtashi ko ya yi hani gareshi a cikin sunnarsa to shi a hukunci kamar abinda Allah Ya haramtashi ne a cikin littafinSa; domin cewa shi ne mai isarwa daga Ubangijinsa.

فوائد الحديث

Girmama sunna kamar yadda ake girmama Alkur’ani kuma a yi riko da ita.

Biyayya ga Manzo ita ce biyayya ga Allah, kuma saba masa shi ne sabawa Allah - Madaukakin sarki -.

Tabbatar da hujjar sunna da kuma raddi akan wanda ya watsar da sunnoni ko ya musanta ta.

Duk wanda ya bijirewa sunna ya yi da'awar takaituwa akan Alkur’ani to shi wanda ya bijire musu ne gaba dayansu, kuma makaryaci ne a cikin da'awar bin Alkur’ani .

Daga cikin hujjojin Annabcinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bada labari game da wani abu da cewa zai faru a nan gaba, kuma ya faru kamar yadda ya bada labarin.

التصنيفات

Muhimmancin Sunna da Matsayinta, Annabtaka, Rayuwar Barzahu