Idann dayanku ya ci abinci to kar ya goge hannunsa har sai ya sude shi.

Idann dayanku ya ci abinci to kar ya goge hannunsa har sai ya sude shi.

Daga Dan Abbas Allah ya yarda da su" Annabi tsira da amincin Allah ya ce: Idann dayanku ya ci abinci to kar ya goge hannunsa har sai ya sude shi.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi mai tsira da amincin Allah ya umarci wanda ya ci wani abinci kada ya goge hannunsa, ko kar ya wanke hannaunsa har sai ya sude shi ko yasa a sude masa domin bai san a ina albarkar abincin take ba, don haka ne Annabi ya yi umarni da sude yatsun, ba mamaki albarka na cikin abin da ya makale a jikin hannaun.

التصنيفات

Ladaban cin Abinci da Shan Abun Sha