Cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- anzo masa da wani Mutum ya sha giya, sai aka yi masa Bulala da zarbar Dabino kwatankwacin Arba'in

Cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- anzo masa da wani Mutum ya sha giya, sai aka yi masa Bulala da zarbar Dabino kwatankwacin Arba'in

An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- "Cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- anzo masa da wani Mutum ya sha giya, sai aka yi masa Bulala da zarbar Dabino kwatankwacin Arba'in"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Wani Mutum ya sha giya a lokacin Annabi SAW sai aka yi masa Bulala da Zarbar Dabino kwatankwacin Bulala Arba’in, Kuma Abubakar –Allah ya yarda das hi- yayyi Bulala ga Mashayin giya a lokacin Halifancinsa kwatankwacin Bulalar Manzon Allah SAW, yayin da lokacin Halifancin Umar ya zo, aka samu bude garuruwa da yawa, Musulmai suka cudanya da wasun su, sai shan giyar ya karu, sai ya Shawarci Malaman Sahabbai akan haddin da zai rika yi musu don ya hana su Shan giyar, kamar yadda haka Al-adarsa take idan Muhimman abubuwa suka faru, da kuma abubuwan da suke bukatar Ijtihadi, saboda Mutane sun karu wajen Shan giya a lokacinsa, sai Abdul-Rahman Bn Auf y ace: kasanya shi daidai da mafi karancin Haddi, shi ne Bulala Tamanin, kuma shi ne Haddin wanda yayi Kazafi, Sai Umar ya sanya shi Bulala Tamanin, to wannan Karin Jan kunne kuma ya danganta da abunda Shugaba ya gani

التصنيفات

Haddin Shan Giya