"Lallai yahudawa sunzo wajen Manzon Allah SAW sai suka gaya masa cewa cewa Mata daga cikinsu da Wani Mutum sunyi Zina

"Lallai yahudawa sunzo wajen Manzon Allah SAW sai suka gaya masa cewa cewa Mata daga cikinsu da Wani Mutum sunyi Zina

An rawaito daga Abdullahi Bn Umar -Allah ya yarda da su- ya ce "Lallai yahudawa sunzo wajen Manzon Allah SAW sai suka gaya masa cewa cewa Mata daga cikinsu da Wani Mutum sunyi Zina" sai Manzon Allah ya ce da su: Mai kuka gani a cikin Attaura gameda Jifa? sai suka ce zamu kunyata su kuma ayi Musu Bulala, Sai Abdullahi Bn Salam ya ce Karya kuke yi a ciki akwai Ayar Jefewa, sukazo da Attaura din aka bajeta, sai dayansu ya dora hannunsa akan Ayar jifewar sai ya karanta wacce takr kafinta, Sai Abdullahi Bn Salam ya ce da shi dauke hannunka sai ya dauke hannunsa, sai ga Ayar Jefewar acikin ta, sai ya ce Yayi Gaskiya Muhammad, saboda yayi Umarni SAW da aje a jefe su, sai aka jefe su din, sai naga Mutumin yana jefe Macen dutse yana kareta"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

التصنيفات

Haddin Zina