إعدادات العرض
Cewa Kuraishawa lamarin Almakhzumiyya datai sata ya damesu
Cewa Kuraishawa lamarin Almakhzumiyya datai sata ya damesu
Ankarbo daga A'isha-Allah ya yarda da ita-"Cewa Kuraishawa lamarin Almakhzumiyya datai sata ya damesu,sai suka ce:Waye zai yiwa Manzan Allah tshira da amincin Allah su tabbata agareshi maganarta?,sai suka ce:Ba wanda zai iya tararsa sai Usama Dan Zaid Masoyin Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai Usama ya gaya masa,sai yace:ka nemi Ceto cikin Hukunci daga Hukunce-Hukuncen Allah?sannan ya tashi yayi huduba,sai yace:Hakika abinda ya halakar da wadanda suke gabaninku cewa su sun kasance idan wani Mai'alfarma daga cikinsu yayi sata sai su rabu dashi,idan kuma Mairauni ne acikinsu yayi sata sai su tsayar da Hukunci akansa,na rantse da Allah:da cewa Fadima yar Muhammad za tayi sata da lallai na yanke Hannunta".Awata ruwayar kuma"Wata Mace ta kasance tana arar kaya sai kuma ta musashi,sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi umarni da a yanke Hannunta"
الترجمة
العربية Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tagalog ئۇيغۇرچە Português മലയാളംالشرح
Wata Mace daga Bani Makhzum ta kasance tana arar kaya daga wajan Mutane da Zamba,sannan ta musashi.Sai wani lokaci ta ari abin ado ta musashi,sai aka sameshi a wajanta,sai lamarinta ya isarwa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai ya nufi zartar mata da Hukuncin Allah Madaukakin Sarki na yanke Hannuwanta,kuma ta kasance Ma'abociyar Alfarma ce,kuma daga Nasaba ta Asali cikin Kuraishu.Sai Kuraishu suka damu da ita da kuma wannan Hukuncin da aka zartar mata,sai sukayi Shawara game da wanda zasu sanya shi Wasida zuwa ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi don yai masa magana ya rabu da ita,basu ga wanda yafi Usama Dan Zaidu ba,domin cewa shi Makusancine Abin so ne ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi.Sai Usama ya gaya masa.Sai yayi Fushi dashi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sannan yace dashi-yana mai inkari agareshi-"ka nemi ceto cikin Hukunci daga Hukunce-Hukuncen Allah"?Sannan ya mike don yayi ma Mutane Huduba ya bayyana musu hadarin misalin wannan ceton wanda zai wofuntar da Hukuncin Allah,kuma saboda maubu'in ya dami da yawa daga cikinsu,sai ya basu Labari cewa sababin halakar wadanda suka zo gabaninmu a cikin Addininsu da Duniyarsu:cewa su suna tsaida Hukunci akan Raunana da Fakirai,sai su dinga barin Karfafa da Mawadata,sai Bala'i ya game acikinsu Sharri da Fasadi suka watsu,sai Fushin Allah da Ukubarsa ta cancancesu.Sannan sai ya rantse tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-kuma shi mai Gaskiyane abin gasgatawa-da cewa wannan aiki zai faru akan Shugabar Matan Talikai Yarsa Fadima-Allah ya tsareta da hakan-da sai ya zartarda Hukuncin Allah Madaukaki agareta.Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi.التصنيفات
Haddin Sata